Gwamnatin tarayya ta sanar da fara rabon metric ton 42,000 na kayan abinci iri-iri a matsayin tallafin da take baiwa ‘yan Najeriya a ranar Laraba.
Alfijir labarai ta rawaito ministan noma da samar da abinci Abubakar Kyari ya shaidawa manema labarai a fadar Gwamnatin Tarayya cewa, tuni aka fara rabon kayayyakin, bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi a Aso Rock Villa da ke Abuja a ranar Laraba.
Shugaba Bola Tinubu ya yanke shawarar sakin metric ton 102,000 na nau’in hatsi daban-daban daga cikin Strategic Reserve da kungiyar Rice Millers Association of Nigeria a Ranar 8 ga Fabrairu, dangane da matsalar karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki a kasar,
“Muna raba wa manyan biranen jihohi tun da farko, saboda kun san irin hadarin da ke tattare da barnatar da kayan abinci, don haka muna aiki da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da sauran hukumomin tsaro na kasa.
“Ina tabbatar muku cewa mun fara rarrabawa a jihohin Arewa maso Yamma, kuma muna raba kashi bakwai ne,” inji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk