Shugaban Karamar hukumar ungoggo Engr. Abdullahi Garba Ramat ya ajiye aikin sa Inda ya mika ragamar tafiyar da karamar hukumar ga Mataimakinsa.
Alfijir labarai ta rawaito Ramat ya shugabanci karamar hukumar ungoggo tun daga shekara ta 2021 zuwa ranar litinin da ya ajiye aikin.
“Alhamdullah, a yau na Mika ragamar tafiyar da karamar hukumar ungoggo ga mataimakina . Na yi iya kokarina na, ta hanyar samar da daruruwan aiyukan raya kasa, na kuma sami lambobin yabo da dama daga ciki har da Gwarzon shugaban karamar hukumar wanda majalisar dokokin jihar kano ta bani. Mu Mun Matsa…” Ramat ya rubuta a shafinsa na Facebook
Ramat wanda ya ajiye aikin nasa cikin wani dan kwarya-kwaryar biki, inda ya bada jari ga mata 500 jari tare kuma da kaddamar da Hatimin karamar hukumar, wanda za a rika amfani da shi a duk wani abu da ya shafi mulkin karamar hukumar.
Tsohon shugaban karamar hukumar ya ajiye aikin ne kwanaki Kadan kafin karewar wa’adin mulkinsu na tsahon Shekaru 3.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V
Allah ya shirye mu