Kungiyar likitocin Asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake jihar Kano ta bayar da Sanarwar janye mambobinta daga bakin aiki har sai abinda hali yayi.
Alfijir labarai ta rawaito rahotanni na nuni da cewa hakan ya faru ne Sakamakon yanda wasu ’yan daba dauke da muggan makamai suka kutsa kai cikin sashin masu kula da masu haihuwa na asibitin inda suka far wa wani likita da ke bakin aiki akan rasuwar yar uwar su a cikin Asibitin kwararru na Murtala Muhammad
Hakan yasa kungiyar likitocin Asibitin suka dauke matakin dakatar da aikin su sabida rashin tsaro a cikin Asibitin.
Haka zalika sanarwar ta kara da cewa Shuwagabannin kungiyar sun tattaru zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka lura da rashin tsaro a duk asibitin. Hakan na kawo cikas ga tsaro da tsaron ma’aikatan lafiya a asibitin.
Kungiyar likitocin Asibitin sun ce za su cigaba da sanya ido kan yanayin tsaro ga mambobin kungiyar yadda ya kamata.
Dan hakan Dukkan membobin mu na kungiyar su sani cewa Wannan sanarwar da aka umarce su da su daina aiki har sai an sanar dasu akan wannan yanayi mara kyau
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V