Daga Baba Usman Gama
Babban sufeton ƴan sanda ya umarci shugabannin ƴan sanda su tsaurara matakan murƙushe ƴan bindiga
Kotun ƙoli za ta sanar da ranar yanke hukuncin zaɓen Sokoto.
Yan bindiga sun halaka jami’a mace yayin da suka kai hari ofishin ƴan banga a Ebonyi.
Ana ci gaba da aikin ceto bayan hatsarin kwale kwale mai dauke da mutane sama da 100 a Jihar Neja.
Gwaman Kano Abba Kabir Yusuf zai kashe N8bn a gina sababbin makarantu 3 masu dauke da kayan aiki na zamani, ta kuma ware kudi domin gyara sauran makarantun firamaren da ake da su.
Wani lauya mai suna Abba Hikima ya ce doka ta hana yin lefe, kayan daki, kayan na gani ina so da sauran tsarabe tsaraben aure ajihar Kano sannan ya ce dokar ta tanadi hukuncin dauri da tara ko kuma kotu ta haɗawa mutum duka biyun
Gobara ta ƙona ‘rumfuna 250’ a kasuwar Fanteka da ke Kaduna.
Kwamitin yaki da shan miyagun kwyoyi da kwacen waya a Jihar Kano ya kafa kotun tafi da-gidanka domin gaggauta hukunta masu laifi.
Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta baiwa al’ummar jihar tabbacin gudanar da sahihin zaben shugabannin kananan hukumomi da za a yi acikin wannan shekarar a jihar.
Wani sanannen wurin sayayya a unguwar Gwarimpa da ke Abuja, mai suna IC World Emporia Centre, ya yi gobara a da sanyin safiyar Laraba.
Za a yi wa faston masu azumin mutuwa a Kenya gwajin ƙwaƙwalwa.
Rikicin kabilanci ya kashe mutane 7 a jihar Nasarawa.
Pakistan ta nemi jakadanta a Iran ya koma gida.
Jirgi ya yi saukar gaggawa bayan fasinja ya gartsa wa ma’aikaciya cizo a Amurka.
Ana taron addu’oi a Nijar kan mutuwar malami a hannun ƴan bindiga.
Shugaban Ukraine Zelensky yace kamata yayi a miƙa wa kasar sa biliyoyin kuɗaɗen Rasha.
AFCON: Morocco tasami nasara akan Tanzania daci 3:0 a wasansu na yammacin yau Laraba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V