Ibtila’I! Shaguna 100 Sun Kone a Gobarar Kasuwar Fanteka a Kaduna

IMG 20240117 193542


Akalla shaguna 100 ne suka kone a wata gobarar da ta tashi a tsakar dare a Kasuwar Panteka da ke garin Kaduna.

Alfijir labarai ta rawaito gobarar ta tashi ne kafin wayewar garin Laraba a Kasuwar Panteka da ke kusa da harabar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere (Kaduna Polytechnic).

Kasuwar Panteka wanda ke kusa da gidan gwamnatin jihar Kaduna a unguwar Tudun Wada, ta yi fice wajen kasuwancin kayan gini da karafa dangoginsu da sauransu.

Sakataren kungiyar ’yan kasuwar Panteka, Ibrahim Muhammad, ya ce gobarar ta fi yin barna a bangaren masu sayar katako.

Ibrahim Muhammad ya ce, “masu gadin kasuwar sun shaida mana cewa ’yan mintoci kadan bayan karfe 12 na dare wutar ta fara ci daga bangaren ’yan katako.

“Sai da jami’an hukumar kashe gobara suka zo daga Jaji aka kashe gobarar da misalin kare 5 na asuba.

“Shagunanmu sama da 100 sun kone, amma yanzu dai ba za mu iya fadan girman asarar da dukiyar aka yi ba,” in ji shi.

Sakataren kungiyar ’yan kasuwar ya kara da cewa ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *