Ola Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, a wani babban taro da Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da Rashawa mai zaman kanta, ICPC, Dr Musa Aliyu ya kaddamar.
Alfijir labarai ta rawaito Shugaban na EFCC na cewar muradin Siyasar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na yaƙi da cin hanci da rashawa, Kamar yadda aka nuna a baya-bayan nan, ya isa ya karfafawa Hukumomi yaki da cin hanci da rashawa damar bayar da gudunmawarsu.
“Munyi imanin cewa tare da irin shugaban da muke da shi, wanda ke shirye kuma a shirye ya ke ya yi abin da ya dace kamar yadda aka nuna a cikin sa’o’i 48 da suka Gabata.
“A bayyane yake cewa Shugaban kasa yana ba da tsarin siyasa da jagoranci don hukumomin yaki da cin hanci da rashawa suyi aiki kuma na yi imanin cewa da wannan, babu wata maboya a gare mu kuma dole ne mu tabbatar da cewa mun ba da mafi kyawun mu.
“Za mu baiwa Shugaban kasa goyon bayan da ya dace kuma mun yi imanin cewa Kwarin Gwiwa zai kasance a wurin don daukar matakan da suka dace.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl