Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Talata 20/06/1445AH – 02/01/2024

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Gwamnatin Najeriya za ta karbe lasisin Karin wasu masu hakar ma’adinai.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutum uku da ake zargin barayin mota ne aka kwato motocin sata a hannunsu a Zariya.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban Karamar Hukumar Akwanga ta Jihar Nasarawa, Safiyanu Andaha.

’Yan bindiga sun harbi wani dan banga tare da raunata wasu mutum 3 a yankin Barangoni da ke Karamar Hukumar Bwari a Abuja.

Masarautar Atyap da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna, ta karrama Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Musa Christopher.

Dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a zaben 2023 a jihar Ribas, Magnus Abe, ya ce zai fice daga jam’iyyar zuwa APC mai mulki.

Gwamnan jihar Gwambe yace APC za ta iya lashe duk kujerun kananan hukumomin jihar yayin zaben da za a gudanar nan ba da daɗewa ba.

Dubban mutane za su kwana a waje bayan wata gagarumar girgizar ƙasa a Japan.

Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasar Japan ya karu.

Shugaban Kasar Rasha Putin ya sha alwashin zafafa kai hare-hare kan Ukraine.

EPL: Liverpool ta sami nasara akan Newcastle da ci 4:2 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *