Suna ihu da harshen Yarbanci, โEbi npa wa ooโ maโana- muna jin yunwa.
Alfijir labarai ta rawaito ranar Jumaโa ne mazauna tsibirin Legas da โyan kasuwa na babbar kasuwar Idumota suka nuna rashin gamsuwa da Shugaba Bola Tinubu, suna ihu da harshen Yarbanci, โEbi npa wa ooโ maโana- muna jin yunwa.
โYan kasuwar da suka yi wannan ihun a bangarorin biyu na titin yayin da ayarin motocin shugaban kasar suka bi ta kasuwar, sun ki yi masa jinjina amma maimakon haka suka ci gaba da magana kan radadin da suke ciki da ake kyautata zaton gwamnati ce ta janyo hakan.
A karkashin koke-koken da ke cikin faifan bidiyon, an ji mazauna garin na cewa fadar shugaban kasar ta san tsare-tsaren mutanen wanda shi ne ya sa aka dauki tsauraran matakan tsaro duk da haka, bai hana mutanen kasuwar nuna damuwarsu ba.
Shugaban ya je Legas ne domin bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Jama a da dama a fadin kasar sun ta kokawa da salon mulkin da shugaban ya fara wanda al ummar ke cewar, bayan fara tsunduma su da tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari ta yi a cikin masifar rayuwa yanzu haka wannan ya zo ya karasa Danna su gaba Daya.
Allah ya ka wo mana sauki da rangeame Ameen.
DAILY POST
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐๐
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl