An gurfanar da matar da ake zargi da kashe abokin Kasuwancin ta a gaban kotun majastiri a Kano

IMG 20231228 063813

An tuhumi Hafsa Surajo da zargin laifin yunkurin kashe kai da kisan kai wanda ya sabawa sashi na 281 da 221 na kundin laifuffukan na kasa a gaban kotun majastiri mai lamba 37 da ke yan kaba

Alfijir labarai ta rawaito, Hafsah Surajo da take hannun ‘yan Sanda tace tayi yin kurin yanka kanta da wuka a gidanta dake unguwa uku inda na’fi’u wanda yaron gidanta yayi kokarin hanata inda ta cakamasa a kirji da sassan jikinsa.

Bayan karanta mata ƙunshi tuhumar ta amsa yunkurin kashe kanta amma ta musanta kashe Na’fi’u.

Mai gabatar da kara barista Lamido Abba Soron Dinkin yayi roko karkashin sashi na 295 ACJL da ajiye ta a gidan gyaran halin da tarbiyya kafin a sami shawarwari daga ma’aikatar Shari’a tun da kotun bata da hurumi.

Mai Shari’a Hadiza Abdurrahaman ta aike da ita zuwa gidan gyaran halin da tarbiyya sai ranar 1 ga watan 2 na shekara mai kamawa 2024.

Barista Rabi’u Sidi shine lauyan dake kare Hafsan a gaban Kotun.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *