Bafarawa Ya Aikewa Shugaba Tinubu Budaddiyar Wasika Kan Tsohon Shugaba Buhari

IMG 20231225 105119

“Abin da ya kamata Shugaban kasa ya sani shine ya Gaji matsala, Kuma bai kamata yayi watsi da ita ba. Ba Shugaba Bola Tinubu ne ya jawo abin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu ba. Tsohon shugaban kasa (Muhammadu) Buhari ya jefa ƙasar a wannan hali da muke ciki

“Idan har shugaba Tinubu zai ci gaba da ayyukan alheri da yake yi, Musamman farfado da wasu ayyuka da aka yi watsi da su a Abuja da sauran yankunan, ban ga dalilin da zai sa Gwamnatin Tinubu ta gagara bincikar Gwamnatin Buhari ba.

“A gaskiya Buhari ne mutum na farko da Yakamata a fara bincike Domin lokacin da ‘yan Najeriya suka zabe shi Buhari ya shaidawa ‘yan Najeriya cewa shi ne mafi gaskiya da adalci, haka a yakin neman zabe, ya ce shi ne mai gaskiya ne, mafi tsafta da sauransu.

Yanzu, ya yi shekaru takwas, kuma ya kammala mulkin sa Yazama Dole a bincike yadda ya gudanar da ayyukan sa.

Don haka, zai zama babban koma Baya idan Tinubu ya gaza binciko Gwamnatin Buhar bai. Idan kuma yana son ya sauka daga zargi, sai ya binciki Gwamnatin da ta shude. Idan aka samu Buhari da tsafta to mutane za su ji dadi da shi. Amma idan aka aka same Shi da laifi dole ya amsa laifin sa

“Amma ba zai yi kyau ‘yan Najeriya su bar Buhari ya tafi haka ba. Idan har shugaba Tinubu ya kyale Buhari ya tafi ba tare da tada kayar baya ba, to ya kamata (Tinubu) ya sani cewa duk abin da Buhari ya yi a lokacin yana Gwamnati, za a ga Tinubu a matsayin wanda ya yi.

“.Meyasa Buhari ya binciki wasu mutane a Gwamnatin Jonathan (Goodluck) me Zai hana Tinubu binciken Gwamnatin Buhari? Na fadi haka ne saboda Buhari ya binciki Gwamnatin Jonathan kuma an kwato makudan kuɗaɗe.

“Abin da wasu jami’an Gwamnatin Jonathan suka sata kadan ne idan aka kwatanta da abin da Gwamnatin Buhari ta yi. Gwamnatin Buhari ta ci bashin kudi sannan suka wawure kuɗaɗen da suka ciyo. Bayan sun karɓi kuɗi, ba mu ga abin da suka kashe kuɗin a kai ba.

“To, me Shugaba Tinubu zai gaya mana? Ko don su Tinubu da Buhari suna jam’iyya daya ne? Don haka, ya kamata Shugaba Tinubu ya yi ƙoƙarin kada ya dauki laifin da ba nasa ba. Dubi tallafin man fetur; Ba Tinubu ne ya cire tallafin man fetur ba, Buhari ne ya yi haka. Shugaba Tinubu karantawa yayi.

“Tsohon shugaban kasa Buhari ya cire tallafin man fetur watanni shida kafin ya bar mulki. Abin da ya faru shi ne bai kara tallafin mai a kasafin kudin ba. Amma Tinubu ya zo ne kawai ya sanar da cire shi, ko da Gwamnatin da ta shuɗe ta cire shi.

“Idan wani ya zargi Tinubu a yanzu, Wannan mutumin bai yi wa Shugaban kasa adalci ba. Don haka ya kamata Shugaban kasa ya yi ƙoƙarin ya zama mai cin gashin kansa domin mutane za su yi masa hukunci bayan ya bar mulki. Amma a yanzu ba zai iya daukar laifin duk abin da Gwamnatin Buhari ta yi ba.

Babu wanda zai zargi Tinubu don ya bincike Gwamnatin Buhari. Idan ba a sami Buhari da laifi ba, aƙalla zai ci gaba da cewa shi mai tsafta ne. Maganar gaskiya ’yan Najeriya ba za su taba yafe wa Tinubu ba idan ya gaza binciken Gwamnatin Buhari.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *