Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a ranar Asabar a wani hatsarin mota a garin Kwanar Gujungu da ke karamar hukumar Taura na jihar Jigawa.
Alfijir labarai ta rawaito mai magana da yawun ƴan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse, a yau Lahadi.
Shiisu ya ce hatsarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe 12:00 na rana, inda motoci biyu, kirar Honda saloon mai lamba NSR 469 AE, da wata motar Golf mai lamba AUY 292 XA suka yi karo da juna.
Ya ce motar Honda na ɗauke da fasinjoji biyar, sai direbanta mai suna Abdullahi Muhammad, yayin da motar Golf kuma ke ɗauke da fasinjoji huɗu, da direban Safiyanu Mamu.
Ya ce tawagar ma’aikatan hedikwatar ‘yan sanda ta Taura sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai waɗanda abin ya shafa zuwa babban asibitin garin Taura, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ahmadu Abdullahi, a madadin sauran jami’an rundunar, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu tare da addu’ar Allah ya gafarta musu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp