Barr Abba Hikima Ya Nuna Rashin Amincewa Kan Gina Gadoji Da kudin Kananan Hukumomi

IMG 20231220 162724

Barasta Abba Hikima Fagge, ya bukaci Gwamnatin Kano da ta duba Allah ta tsayar da aikin gadojin da ta kuduri aniyar yi a Kano ta hanyar ɗibar kudaden kananan hukumomi don gina gadoji a birni alhali kauyuka na cikin matsanancin hali da bukatar aiki.

Alfijir labarai ta rawaito Abba Hikima ya bayana hakan a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Laraba inda mabiyansa ke ci gaba da bayana ra ayoyinsu kan kalaman nasa.

Hikima ya ce, “Irin wadannan abubuwan da ake dauko wa,su ke sawa mutane suke daukar gaba daya bangaren na ‘yan siyasa.

Takardar da aka fitar don fitar da kudaden kananan hukumomi don gina gadar Dan Agundi

“Yanzu saboda Allah ina adalci anan? Kauyukan Kano suna cikin mugun hali, kwanaki Freedom Radio ta yi ta bankado matsalolin kauyukanmu amma a dauko kudinsu a saka a gada guda daya Me wannan kudin?”

“Lallai akwai wani abu da yake faruwa a kasa.” cewar Abba Hikima.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *