Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Talata 05/06/1445 – 19/12/2023

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Gwamnatin tarayya ta ce ta fahimci girman ƙalubalen tsaron da ke gabanta tare da alƙawalin kawo ƙarshen matsalar zuwa karshen 2024.

Babban hafsan tsaro ya ce ana dab da kammala bincike kan harin bam ɗin Tudun Biri na Kaduna.

’Yan bindiga sunyi awon gaba da hakimin Rakyabu, Magaji Sa’idu da kuma babban limamin kauyen, da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

BUA zai gina kamfanin samar da tan 700 na gas kowacce rana a Najeriya.

Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar nasarar tsoffin gwamnonin jihar Sakkwato Wamako da Tambuwal a matsayin Sanatoci.

Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bayyana cewa bai umurci ma’aikatan gwamnati a jihar su daina sanya tufafin gargajiya da suka hada da babbanriga da kaftani zuwa ofis ba.

Wani Sufeto a rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ya kashe kansa bayan da aka ce ya harbe abokin aikinsa Monday Gbaramana har lahira.

An kama wani bakanike mai shekara 25 yana kokarin sayar da motar wani mutum da ya ba shi gyara a Legas.

Bayanai daga Taraba na cewa an sace mutum 21 har da sarki mai daraja ta lll na al’ummar Pupule, Alhaji Umaru Nyala a ƙaramar hukumar Yorro da ke jihar.

An kama mutum biyu da ake zargi da bai wa masu garkuwa kariya a yankin Gumel ta jihar Jigawa.

Jami’an yan sanda sun kama wani magidanci kan zargin kashe matarsa saboda ta ki girka abincin da ya fi so a yankin Olota da ke karamar hukumar Alimosho ta jihar Lagas.

Tsohon Ministan wutar lantarki Olu Ogunloye da ake nema ruwa a jallo ya shiga hannun EFCC.

An gurfanar da wasu manoma shida bisa zargin kashe makiyayi da shanun sa 97 a Kano.

’Yan Najeriya 260,000 sun nemi yin hijira su bar kasar, a cewar Hukumar ’yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Ana fargabar tashin farashin man fetur bayan hare-hare a tekun Maliya.

Mutum fiye da 100 sun mutu sakamakon girgizar ƙasa mafi muni a China.

Afirka ta Kudu za ta hukunta ‘yan kasar da ke taimakawa Isra’ila yaki a Gaza.

Hukumar kwallon kafar Ingila taci tarar Man. City fam dubu 150 sabida kawanya da yan wasan suka yiwa alkalin wasa yayin wasan da sukayi canjaras 3:3 da Tottenham a farkon wannan watan.

Tsohon Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ya gargadi mahukuntan kungiyar game da wasu mutane da kuma ’yan wasa wadanda ya ce su ne matsalarta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *