AROGMA ta yabawa NNPC na Dakile Layukan Mai a Watan Disamba

IMG 20231119 140840

Kungiyar dillalan man fetur da iskar gas ta Arewa (AROGMA) ta yabawa mahukuntan kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL bisa yadda suka samar da man fetur a kan lokaci a karshen shekara ta 2023, inda suka tabbatar da rashin samun layin mai a watan Disamba.

Alfijir labarai ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata tattaunawa da Alhaji Bashir Ahmad Danmalam, shugaban kungiyar AROGMA da manema labarai a ofishin sa.

Danmalam ya kara da cewa rashin layukan man fetur a watan Disamba na nuni da gagarumin ficewa daga ukubar da alumma suke fuskanta a baya, inda mutane suke dadewa suna jira ko ma su shafe kwanaki suna layi a karshen shekara.

Bashir ya tabbatar da wannan nasarar ne ga kokarin hadin gwiwa na Adedapo Seguna, mataimakin shugaban kamfanin na Downstream NNPC, da kuma Lawal Sade, Manajan Darakta na Kamfanin Kasuwancin NNPC, wadanda suka yi aiki tare domin tabbatar da samar da mai cikin gaggawa a shekarar da ta gabata.

Ya kuma tabbatar wa β€˜yan Najeriya a madadin kungiyar AROGMA da duk masu ruwa da tsaki cewa babu bukatar a firgita, kuma za su iya yin bukukuwan Kirsimeti da Sallah da sabuwar shekara ba tare da layukan man fetur ba.

Danmalam ya Kara yabawa matuka da kokarin da aka yi, yana mai jaddada nauyin da ke wuyan bangaren da ke da alhakin sauke nauyin Al’umma cikin gaggawa.

A kokarin da Adedapo Seguna ya jagoranta, ya nuna iyawarsa kan aikin da ke hannun sa.

Danmalam ya kara da cewa saboda wannan ci gaban da aka samu, yanzu mutum na iya tuka mota daga Legas zuwa Maiduguri a Borno ba tare da fuskantar layukan man fetur ba.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *