Takaitattun Labaran Duniya Na Ranar Laraba 13/12/2023 – 29/05/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Ministan ma’adanai, Dele Alake, ya yi ikirarin cewa wasu ƴan Najeriya masu haƙo ma’adinai ba bisa ka’ida ba ke ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a ƙasar nan.

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutum shida a Gusau, sakamakon wani hatsarin mota.

An kwantar da daliban wata firamare su 18 a asibiti bayan da suka ci abincin da Gwamantin Jihar Osun take ciyar da dalibai a makarantu.

Ministar jin kai da walwala ta koka kan yadda aka ba ta kudade kalilan na kasafin ma’aikatarta

’Yan bindiga sun kashe sojoji hudu da suke rakiyar wasu ma’aikatan kamfanin mai a Jihar Ribas.

An tayar da jijiyoyin wuya a zauren Majalisar Dokokin Kano, kan kudaden da gwamnatin jihar ta ware wa masarautu a karamin kasafinta na 2023.

’Yan sanda sun tsare Daraktan Ma’aikatar Ruwa ta Kano kan zargin karkatar da injinan rarraba ruwan sha a jihar.

Kotu ta ce ɓangaren Fubara ya ci gaba da jagorancin majalisar jihar Ribas.

Kasashe 193 sun kada kuri’a kan kudirin bukatar tsagaita wuta a Gaza.

Manyan kungiyoyin agaji na yi wa ECOWAS matsin lamba kan Nijar.

An kashe karin sojojin Isra’ila takwas a Gaza, daga ciki har da mai mukamin Laftanar Kanal da kuma wani Manjo.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Isra’ila ta fara rasa goyon bayan da take samu a fadin duniya.

UCL: Ancire Manchester United daga gasar bayan rashin nasara a hannun Bayern Munich da ci 1:0 a wasan jiya.

UCL: Real Madrid ta sami nasara akan Union Berlin da ci 3:2 a wasan jiya.

UCL: Benfica ta sami nasara akan Salzburg da ci 3:1 aa wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *