Daga Rukaiyya Umar G/Kaya
Taron ya duba irin wahalar da ake sha wajen hukunta wadanda ake samu da aikata laifin cin zarafin, tsayawa tsayin daka ke kawo aiwatar da hukuncin cikin sauki. In Ji Barasta
Alfijir labarai ta rawaito Shugabar kungiyar lauyoyi mata ta Najeriya, reshen jihar kano, Barrister Bilkisu Ibrahim Suleiman, ce tayi kiran, ta kara da cewar lamarin ya kasance abin kaicho a tsakanin al umma.
Wanan na kunshe ne cikin bayaninta yayin taron ranar da aka yiwa lakabi da saka jari don dakatar da cin zarafin bil adama na wannan shekarar.
Taron ranar ya kuma nuna yadda masu shari a ke-fama dakalubale wajen tabbatar da kare al umma.
Barrister Bilkisu ta bukaci hada hannu wajen yaki da al amarin, tana mai cewa akwai bukatar fito da sabbin dabaru don samun nasarar abinda aka saka a gaba.
Haka zalika taron ya duba irin wahalar da ake sha wajen hukunta wadanda ake samu da aikata laifin cin zarafin, tsayawa tsayin daka ke kawo aiwatar da hukuncin cikin sauki. In Ji Barasta
Baya ga katsalandan da sashen shari a ke ffuskanta wajen yaki damummunar ta adar, Barrister Bilkisu ta kuma kara da cewa tsaikon da akan samu kafin yanke hukunci na jawowa shari ar kaucewa daga wata matsaya da aka nufi aiwatar da ita.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo