NJC Ta Dakatar Da Alkali Kan Yanke Hukunci Ta Hanyar Da Ba Ta Dace Ba

IMG 20231208 113029

An kuma samu Jastis Falola da laifin sauraron shari’a mai lamba HIK/41/2018, wadda ba shi da hurumi a kai, ba tare da ya samun takardar hukuncin daga Babbar Kotun Jihar Kwara ba.

Alfijir labarai ta rawaito Hukumar Shari’a ta Kasa (NJC) ta dakatar da Mai Shari’a S.O Falola na Babbar Kotun Jihar Osun tare da neman a yi masa ritayar dole kan laifin saba ka’idar aiki da kuma bayar da umarnin kotu ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukumar NJC ta kuma kafa kwamitoci 11 domin bincike kan wasu alkalai 51 da ta samu takardun korafi a kansu.

Sakataren yada labaran NUJC Soji Oye ya ce an dakatar da Falola ne sai abin da hali ya yi, a yayin da take jiran abin da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, zai yi kan shawarar ritayar dolen.

Soji Oye ya ce NJC a taronta na 104 a Abuja, ta samu Mai Shari’a S.O. Falola da lafin ba da umarnin biyan N283,174,000 ga Bankin Polaris da wata bukwar hanya.

An gano laifin nasa ne bayan takardar korafin da Bankin Polaris da wani mai suna Dapo Kolapo Olowo suka aike wa NJC kan lamarin.

An same shi da laifin ba da umarnin cire kudaden daga asusun bankin masu kara maimakon asusun wanda ake kara — ainihin wadanda umarnin ya shafa.

An kuma samu Jastis Falola da laifin sauraron shari’a mai lamba HIK/41/2018, wadda ba shi da hurumi a kai, ba tare da ya samun takardar hukuncin daga Babbar Kotun Jihar Kwara ba, kuma ba tare da takardar shaidar rajistar shari’ar a Jihar Osun ba — inda yyake da hurumi.

Soji Oye ya ce a taron NJC karo na 104 a Abuja, karkashin jagorancin Shugaban Alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ya yi watsi da bukatar Gwamna Adeleke na neman rantsar da rantsar da mukaddashin babban alkalin jihar.

Gwamnan ya nemi amincewar NJC ne bayan samun korafi kan Babban Alkalin jihar, Oyebola Adepele-Ojo da kuma matsayar da majalisar jihar ta cimma na dakatar da shi.

Soji Oye ya ce a taron NJC, ta kafa kwamitoci 11 domin bincikar alkalai 51 da ta samu korafi a kansu.

Amma kuma, bisa rahoton kwamitocin binciken wasu alkalai da ta kafa a baya, ta yi watsi da korafe-korafen da aka shigar kan wasu alkalai saboda rashin hujjoji ko janyewar masu korafin.

Alkalan da aka wanke su ne Babban Alkalin Jihar Akwa Ibom, Jastis Ekaete F. F. Obot; Jastis Benson Anya na Babbar Kotun Jihar Abia; Jastis Z. B. Abubakar na Babbar Kotun Tarayya; Jastis Opufaa Ben-Whyte da kuma Augusta Uche K. Chuku na Babbar Kotun Jihar Ribas.

Aminiya

IMG 20231207 WA0244 1
Alfijir Foundation

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

2 Replies to “NJC Ta Dakatar Da Alkali Kan Yanke Hukunci Ta Hanyar Da Ba Ta Dace Ba

  1. Wan nan Abu DS NJC Take yayi dai domin kawo gyara GA fanin shari,a a kasa ta,da mitumcinta yazube a idon Yan kasa da duniya baki daya.

  2. Aslm Alfijir Wan nan abu da NJC Suka dauko yayi daidai ainun,Dankuwa fannin Sharia a kasan nan mutumcinsu yagama zubewa A idon Yan kasa da na baki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *