Khalifan Tijjaniyya a Nigeria, Malam Muhammad Sanusi II, ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta bayyana sakamakon binciken kisan’yan Maulidi da akayi a jihar Kaduna, domin yace an taba samun irin haka a jihar Nasarawa, daga bincike shikenan abin ya sha Ruwa.
Cikin wani bidiyo da aka wallafa a ranar Talata, Khalifan ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da kira gare ga Gwamnati da ta tabbatar ta bada kulawa ga wadanda suka jikkata da kuma adalci ga wadanda suka rasu.
A ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023, rundunar soji ta sakar wa masu maulidin bama bamai a Garin Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, inda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, dukda dai daga baya rundunar ta ce an kai harin ne bisa kuskure.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp