An sayar da Bitcoin a kan $40,700 da misalin karfe hudu na safe a agogon GMT ranar Litinin.
Alfijir labarai ta rawaito farashin kowanne kudin kirifto na Bitcoin ya kai $40,000 ranar Litinin din nan a karon farko tun watan Mayun shekarar da ta gabata, bayan da masu mu’amala da shi suka samu kwarin gwiwa cewa nan ba da jimawa ba Amurka za ta bari a rika amfani da shi wajen harkokin kasuwanci.
Darajar kudin na kirifto ta tashi sosai a wannan shekarar, inda ta ninka da kusan kashi 150, bayan da mutane suka samun kwarin gwiwa cewa nan gaba kadan hukumomin da ke sanya ido kan hada-hadar kudi za su bari a soma amfani da shi.
Hakan zai sa a rika bibiyar farashin kudin na bitcoin da kuma barin jama’a su sanya hannun-jari a cikinsa kai-tsaye.
“Wannan manufa ta amfani da wannan kudi a kasuwanni hannun-jari… ana sa rai sosai kuma hakan zai daukaka darajar bitcoin,” in ji Lucy Guzmararian, mai kamfanin Token Bay Capital, a hirarta da Bloomberg.
An sayar da Bitcoin a kan $40,700 da misalin karfe hudu na safe a agogon GMT ranar Litinin.
AFP
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp