Kotu ta  daure wani dan yahoo kan zargin lalata da wata budurwa har sai da ta mutu

Screenshot 20221014 081451 com.android.chrome edit 14830240241485

Kotu ta tisa keyar wani mai damfara ta intanet dan shekara 19 zuwa kurkuku kan zargin lalata da wata budurwa har ta mutu a Jihar Kwara.

Alfijir labarai ta rawaito ’Yan sanda sun shaida wa kotu cewa matashin da ake zargin ya yaudari budurwar mai shekara 17 ne zuwa wani otel a garin Ilori, ya yi mata fyade har ta mutu.

Dan sanda mai gabatar da kara, Abdullah Sanni, ya shaida wa kotun cewa matashin ya yi kokarin tsere daga otle din, amma manajan otel din ya tsare shi, saboda bai biya kudin dakin da ya kama ba.

“Daga bisani manajan otel din ya bi shi zuwa dakin inda aka ga budurwar kwance a cikin jini ba ta motsi.

Matashin ya shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa shi dan damfara ta intanet ne kuma, ya sadu da budurwar, wanda a dalilin haka ne ta fara fitar da jini har ta mutu.”

Daga nan ne alkali Muhammad Dasuki ya ba da umarnin a tsare matashin a gidan yari, ya kuma dage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan nan na Disamba.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *