Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Asabar 02/12/2023CE – 18/05/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Kasafin kuɗi na 2024 ya tsallake karatu na biyu a majalisun ƙasa.

Hakimai 3 sun mutu a hatsarin mota a jihar Oyo.

Shugaban kamfanin BUA Abdul Samad Rabiu ya yi watsi da mukamin da aka ba shi na mamba a kwamitin kudi na Jam’iyyar APC.

Wasu tsoffin ma’aikatan Gwamnatin Kano da suka yi ritaya a 2016-2020 za’a fara biya kudadensu na fansho da garatuti Naira biliyan shida.

Malaman wucin-gadi na shirin J-Teach a Jigawa sunyi zanga zanga kan zargin gwamnatin jihar da neman fakewa da shirya musu sabuwar jarabawar gwaji da nufin maye gurbinsu.

Hukumar DSS ta yi fatali da jita-jitar cewa daraktan hukumar, Alhaji Yusuf Bichi ya handame kudaden rage radadi na ma’aikata.

Shugaban jami’ar ABU, Farfesa Kabir Bala ya bukaci ayi bincike domin gano abin da ya haddasa gobarar.

Ƴan ta’addan ISWAP sun kashe ƴan sakai mutum 2 a wani harin da suka kai a ƙauyen Katarko kusa da Gujba a jihar Yobe.

Shugaban Faransa zai je Qatar don tattaunawa rikicin Falasɗinawa da Isra’ila.

Dakarun juyinjuya halin Iran sun ce harin Isra’ila a Syria ya kashe mambobinsu.

An umarci jami’an Isra’ila su bar Qatar bayan tattaunawa ta tsaya cak.

EPL: Arsenal ta sami nasara akan Wolves da ci 2:1 a wasan yau.

Laliga: Girona ta sami nasara akan Valencia da ci 2:1 a wasan yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *