Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta jihar Kano ta yanke.
Alfijir labarai ta rawaito a baya kotun ta tabbatar da nasarar ga Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC, Inda ta ce shi ne ya lashe zaben majalisar dokokin jihar na kananan hukumomin Kunchi/Tsanyawa ba dan takarar jam’iyyar NNPP Muhammad Yusuf Maigado ba.
Bugu da kari, kotun daukaka kara ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe inda aka soke ƙuri’u ko kuma aringizon kuri’u cikin kwanaki 90 daga ranar da za a yanke hukunci kamar yadda justice watch ta wallafa.
Idan za’a iya tunawa tun bayan da hukumar zabe ta INEC ta ayyana Gwarmai a matsayin wanda ya lashe zaben, lauyan masu shigar da kara, Barista Abba Hikima, ya nuna rashin jin dadinsa inda ya kai karar kotu .
Hikima ya kara da cewa INEC ta tafka kura-kurai a shari’a ta hanyar bayyana sakamakon zabe a lokacin da ba a kammala zaben ba, kuma an tafka kura-kurai da dama da suka hada da soke sakamakon zabe, lalata akwatunan zabe, da kuma kura-kurai daban-daban na zabe.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp
State Assembly ai Gwarmai