Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Litinin 27/11/2023 – 13/05/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu zai gabatar wa majalisa kasafin kuɗi na 2024.

Alkalin alkalan Najeriya ya nemi alkalai su kare mutuncin shari’a.

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin warware matsalar tashin farashin gas.

Kakakin Rundunar Sojin Sama, Air Kwamado Edward Gabkwet ya ce sun samu nasarar kashe manyan kwamandojin Boko Haram ciki har da na hannun daman Shekau, Abu Asad.

Sojoji sun kubutar da mutum biyu daga hannun ’yan bindiga a Taraba.

Sojoji sun ceto wasu mutane da ‘yan bindiga suka sace a jihar Kebbi.

Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nada Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma’a’ikatan gwamnatin jihar.

Kotun daukaka kara ta ta kwace kujerar kakakin Majalisar jihar Kaduna Yusuf Dahiru Liman na APC inda ta umarci sake zabe a mazabu biyar.

Shugaban Jam’iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas, ya bai wa Kwamishinan Shari’ar jihar, Haruna Isa Dederi wa’adin awa 48 ya janye kalaman zargin bayar da cin hanci da shugabannin APC suka yi dangane da shari’ar zaben gwamnan jihar.

Wani Sifetan ‘yan sanda ya rasa ransa a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a jihar Kebbi.

Gwamnatin Lagos ta murkushe babura dubu daya da dari 500.

Bayan shafe tsawon shekara uku ana gyaran Kasuwar Barci da ke a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, gwamnatin jihar ta sake bude kasuwar.

An shiga rudani yayin da fasinjojin wani Jirgin sama suka da ke shirin zuwa Abuja kwatsam sai suka tsinci kansu a Asaba.

Guguwa mai karfin gaske ta katsewa kauyuka sama da 2000 lantarki a Rasha.

Kasashen duniya na bukatar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas.

Hankula sun tashi a Kenya bayan gano gawa 4 a wata gonar masara.

Al’amura sun fara daidaita a Saliyo bayan yunkurin kifar da gwamnatin kasar.

Tashar samar da lantarki daga hasken rana a Nijar ta fara aiki.

Shugaban Saliyo ya ce an cafke mutanen da suka kai hari barikin soji a Freetown.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *