Babbar kotun tarayya mai lamba biyu dake zaman ta a unguwar Gyadi-gyadi kano, ta gargadi wani lauya Yahaya Isah Abdurrashid dake aiki a chambar Dikko & Mahmud kan ya gabatar da wanda yake karewa a gaban ta a ranar 6 ga watan Disamba da muke ciki.
Alfijir Labarai ta rawaito tun da fari dai babban sifeton’yan sandan kasar nan Kayode Egbetukun ne ya yi karar wani Dan kasar Labanon Mai suna Maged Ali Taan tare da wani dan kasar nan Mustafa Tiamiyu a kotun da tuhumar hada kai wajan aikata laifi tare da cinnawa wani gida mai lamba 5C dake kan titin Murtala Muhammad a nan Kano wuta. Tin a shekarar 2021.
An zargi sun cinnawa gidan wuta ne saboda kwadayin za su karbi makudan kudaden inshora, sai ƴan sanda suka ta da ballin su. Bayan kuma haya suka kama gidan.
Lokacin da suke wajan ‘Yan sanda ne lauyan ya karbe su beli, a zaman kotun na wannnan ranar ɗan kasar wajan bai hallacci kotun ba, kuma koda aka tambayi lauya Yahaya sai ya ce bashi da lafiya ne, daga bisani kuma ya ce ai tsoron zuwa kotun yake.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
A nan kotun ta ja hankalin sa kan cewa fa shi lauya ne, kuma masanin doka, dan haka aka daga zuwa ranar 6 ga watan Disamba mai kamawa na wannnan shekarar ta 2023.
Bayan fitowa daga kotun mun so jin ta bakin lauya Yahaya Isah amma yaki cewa komai haka shima lauyan ‘yan sandan Abdussalam Dan mai daki bai magantu ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp