Hukumar Da’ar Ma’aikata, CCB, ta ce ta gurfanar da Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin-Gado, a gaban kotun da’ar ma’aikata da ke Abuja, bisa tuhume-tuhume 10.
Alfijir Labarai ta rawaito hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugabar yada labarai ta CCB, Veronica Kato ta rabawa manema labarai a Abuja a yau Asabar.
Kato ta ce laifukan da ake tuhumar Muhuyi sun hada da karya dokokin hukumar na jami’an gwamnati da cin hanci da rashawa, bata sunan ofis, bayyana kadarorin karya, cin hanci, karbar kyaututtuka da sauransu.
Ta ce an gurfanar da Muhuyi a gaban kotun a ranar Alhamis.
Ms Kato ta ce bincike ya nuna akwai wasu asusun ajiyar banki da ba a bayyana ba da kudadenhar har Naira miliyan 394, wanda hakan ya sa ake zargin almundahana.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Ta ce duk da haka an bayar da belin wanda ake kara akan kudi Naira miliyan 5 da kuma mutum biyu masu tsaya masa da ke da kadarori a babban birnin tarayya Abuja.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp