Tirka-Tirka! An Sace Wayar Tsohon Minista A Cikin Kotun Abuja

ALFIJIR 1

Maku dai ya je kotun ne don raka dan takarar Gwamnan Nasarawa na PDP

Alfijir Labarai ta rawaito wasu da ake zargin barayi ne a ranar Laraba sun sace wayar tsohon Ministan Watsa Labarai, Labaran Maku a kotun daukaka kara da ke Abuja.

Ana zargin an sace wayar ne yayin zaman kotun, jim kadan bayan ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan Jihar Nasarawa.

Kotun dai ta soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wacce ke sauraron karar da Gwamnan Jihar, Abdullahi Sule, ya shigar, yana kalubalantar nasarar da kotun sauraron kararrakin zabe ta ba dan takarar PDP, David Umbugadu.

Labaran Maku dai na ɗaya daga cikin kusoshin jam’iyyar PDP da suka rufa wa Umbugadu baya yayin zaman kotun.

Sai dai bayan an kammala zaman kotun, an ga Labaran Maku ya koma gefe yana tambayar ko akwai wanda ya ga wayar tashi.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Amma duk kokarin da hadimai da magoya bayansa suka yi na neman wayar a harabar kotun, ya ci tura.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *