Hukumar Tace Fina-finai ta dakatar da Jarumi Abdul Saheer da aka fi sani da Malam Ali Kwana Casa’in daga Fina-finan Hausa har tsahon Shekaru biyu.
Alfijir Labarai ta rawaito hukumar tace hakan ya biyo bayan korafe-korafen da aka yi a kansa na cewa yana yada bidiyon batsa a kafafen sada zumunta.
Shugaban hukumar Abba El-Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
El-Mustapha yace Hukumar ta gayyaci Jarumin domin ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa na yada bidiyon batsa, amma ya bijirewa amsa gayyatar .
” Abun da Jarumi yayi na kin amsa gayyatar da mukai masa na zuwa gaban hukumar da karfe 10 na safiyar yau ( Litinin) ya nuna cewa yayi abun da yayi don ya ci mutuncin al’ummar jihar kano da kuma zubar da kimar ta”. El-Mustapha
Shugaban hukumar tace fina-finai ya kuma yi kira da dukkanin masu shirya fina-finai da su guji sanya Jarumin a fina-finan su har sai wa’adin da hukumar ta sanya masa na shekaru biyu ya cika.
” Haka zalika Muna kira ga kafafen yada labarai da su daina gayyatar Jarumi Abdul Sahir wadanda aka fi sani da Malam Ali don yin hira da shi akan duk abun da ya Shafi harkokin fina-finai”. Inji Abba El-Mustapha
Shugaban ya kuma bukaci duk wadanda dama sun sanya Jarumin a fina-finan su amma basu saki fim din ba ,da su hanzarta Kai fina-finan na su Cikin sati biyu domin tantancewa.
Sai dai yace duk wanda ya wuce sati biyu bai kai fim din sa ba to ya sani ba zasu saurare shi ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp