Daga Baba Usman Gama
Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya nemi Majalisar Tarayya ta mayar da lokutan zaɓen gwamna lokaci ɗaya a duk fadin ƙasa.
Jirgin ruwa ya kife da ma’aikatan zaɓe a Bayelsa
INEC tace suna bincike kan takardun sakamakon zaɓe da aka cike kafin fara zaɓe a jihar Kogi
Wasu ’yan bangar siyasa sun bude wa jama’a wuta tare da sace kayan zabe a yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Bayelsa.
Jami’an tsaro sun daƙile yunƙurin garkuwa da jami’in zaɓe a Owerrin jihar Imo.
’Yan banga sun hallaka wasu ’yan bindiga 3 da suka addabi yankin Ngaski da ke Jihar Kebbi da satar mutane.
Wasu mutane ɗauke da sanduna na korar ‘yan jarida daga rumfar zaɓe mai lamba 200 Unit Estate da ke birnin Lokoja na jihar Kogi.
Daya daga cikin masu sanya idanu a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa ya ce sun ga yadda aka riƙa sayen ƙuri’un jama’a a lokacin zaɓen.
Masarautar Bauchi ta tube rawanin wasu sarakai shida a yankin Hakimin Galambi.
Hisbah ta cafke mutum 37 kan karuwanci da sayar da giya a jihar Yobe.
Jihar Imo 2023: jaridar Leadership ta rawaito Yan daba sun afkawa jami’an APC dake siyan kuri’u, sun kwace musu miliyan 1.5.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar kakakin majalisar jihar Gombe, Honarabul Abubukar Luggerewo.
Yayin da ake murnar yafe basukan kwastomomi, kamfanin MTN ya ce tabbas an goge basukan amma hakan matsalar na’ura ce ta jawo.
Shugabannin Gabas ta Tsakiya sun cacaki Isra’ila a kan yadda take ragargazar Gaza.
Saudi Arabia zata zuba jari a matatun man Najeriya guda 4 domin farfado da su.
Yariman Saudiyya ya yi Allah-wadai da Isra’ila.
Rasha ta harba makami mai linzami zuwa Kyiv babban birnin Ukraine.
EPL: Manchester United ta sami nasara akan Luton Town da ci 1:0 a wasan yau.
EPL: Arsenal ta sami nasara akan Burnley da ci 3:1 a wasan yau.
EPL: Wolves ta sami nasara akan Tottenham da ci 2:1 a wasan yau.
Bundesliga: Bayern Munich ta sami nasara akan Heidenheim da ci 4:2 a wasan yau.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp