Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Alhamis 09/11/2023 – 25/04/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Gwamnatin Najeriya ta soki zanga-zangar NLC da TUC a filin jirgin saman Abuja.

Bom ya kashe kwamandojin Civilian JTF da dakarunsu a Borno.

Kungiyar Lauyoyi ta Kasa a Jihar Gombe (NBA) ta yi Allah-wadai da harin da wasu suka kai wa alkalin babbar kotun jihar tare da ma’aikatansa.

An tsinci gawar wata matashiya ‘yar shekara 18 mai suna Waliyah a wata rijiya a Jihar Kwara.

Akalla mutane 11 suka rasa rayukansu yayin da ƴan bindiga suka kai sabon farmaki a kauyuka 2 da ke yankin Gandi a ƙaramar hukumar Rabbah a jihar Sakkwato.

Kotun daukaka kara ta mayar da dan majalisar jihar Taraba, Honarabul Nuhu Akila na jam’iyyar PDP kujerarshi.

Jibi ranar 11 ga watan Nuwamba, Kotun ɗaukaka ƙara zata fara zama kan zaben Gwamnan Filato.

Cutar Diphtheria ta kama mutum 6 a Gombe.

Dattawan Arewa sun ce za su sasanta Dangote da AbdusSamad BUA.

An jibge jami’an tsaro a sassan jihar Kogi gabanin zaben gwamna da za a yi ranar Asabar.

Tsohon gwamnan CBN, Emefiele ya koma gida bayan shafe kwana151 a tsare.

Kungiyar Jihadin Falasɗinawa ta saki bidiyon ‘yan Isra’ila da take garkuwa da su.

Harin jirgi maras matuki ya faɗa kan birnin Eilat na Isra’ila.

An soma taron jin kai kan Gaza a birnin Paris na kasar Faransa.

Hukumomi na neman mutanen da suka sare bishiya mai tsarki a Ghana.

Chadi ta amince da yin afuwa ga masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a bara.

Ƴan Laberiya na shirin shiga zaɓe zagaye na biyu ranar Talata.

Gwamnatin soji a Myanmar ta rasa iko da yankuna da ke kan iyakarta da China.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *