Wasu daga cikin ayyukan sun hada da Gina gadar sama da ta kasa a Dan Agundi da Gina gadar sama a Sha tale-talen Tal’udu
Alfijir Labarai ta rawaito majalisar zartaswar jihar Kano a zamanta na 8 a karkashin jagoranci Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta amince da cire Naira Biliyan 40, domin gudanar da Wasu muhimman ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.
Ayyukan sune:
- Gina gadar sama da ta kasa a Dan Agundi.
- Gina gadar sama a Sha tale-talen Tal’udu.
- Inganta hanyoyi tare da gina rufaffun magudanan ruwa a hanyan Jakara – Kwarin – Gogau.
- Gina titin Kofar Waika – Unguwar Dabai – Yan Kuje Western Byepass.
- Gina mahadar Unguwa Uku – Yan awaki – Limawa.
- Kammala hanyar Kanye – Kabo – Dugabau a karamar hukumar Kabo.
- Kammalawa tare da fadada titin Kofar Dawanau – Kwanar Madugu izuwa hannu biyu.
- Sake bayar da kwangilar aikin gadojin masu tafiyar kafa, a wurare daban-daban a fadin jihar Kano.
- Gyaran fitilun kan tituna da fitilu masu bada hannu, dake cikin birni.
- Karasa biyan kudi tare da dawo da aiki gadan-gadan na kwangilar gyaran hanyar Kwanar Kwankwaso a karamar hukumar Madobi.
- Aikin gyare-gyare a Makarantar Kangararru dake Kiru.
- Sayan kayayyaki da magunguna domin baiwa cibiyoyin kiwon lafiyar jama’a damar samar da tsarin kulada masu hatsari, da mata da yara kyauta.
- Biyan magunguna da sinadarai da kayan masarufi da aka kawo wa asibitin yara na Hasiya Bayero.
- Kammala biyan kudin shirin gwamnatin jihar Kano zagaye na Uku na allurar rigakafin cutar mashako, a kananan hukumomi 22.
- Sake gina babban dakin Karatu da ya kone a kwalejin nazarin shari’a ta Aminu Kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp