Kotu ta dakatar da Gwamnatin Kano Kama Musa Iliyasu Kwankwaso

Screenshot 20221202 154709 com.facebook.katana edit 16234138425645

Babbar kotun tarayya dake zaman ta a jihar kano ta bada umarnin hana kama wanda ya shahara nan wajen yiwa gwamnatin jihar kano ta jam’iyyar NNPP adawa Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso.

Alfijir Labarai ta rawaito tun bayan da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan kano ta ce Nasiru Gawuna ne gwamnan Kano ba Abba Kabir Yusuf ba, Musa Iliyasu Kwankwaso yake yiwa gwamnatin bankada tare da yin wasu zarge-zarge na cewa gwamnatin tana ranto kudaden domin ta tafi ta bar su da biyan bashi.

Musa Iliyasu Kwankwaso ne dai ya shigar da karar gwamnatin jihar kano da kwamishinan yan sanda na jihar kano, tare da rokon kutun da ta hana wadanda yake kara kama shi har sai kotun ta ji bahasin dalilin da yasa suke son kama shi.

A cikin Umarnin kotun mai kwanan watan 25 ga watan October, 2023, Kotun ta bukaci wadanda ake kara da kada su kama mai Kara (Musa Iliyasu Kwankwaso) , sannan kowa ya tsaya a matsayinsa har sai kotun ta sauraren dukkanin bangarorin Shari’ar.

Kotun dai ta ce zata fara sauraron karar ne a ranar 07 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Kadaura24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *