PCACC ta kama wani da ake Zargi da sayar da Filayen Gwamnati Na Naira Biliyan 2.3 a Kano

📸Anti Corruption

Hukumar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kama wani Musa Salihu Ahmed da laifin sayar Filayen Gwamnati Kimanin Guda 632 Ga Mutane daban-daban a faɗin Jihar Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban PCACC Muhuyi Magaji ya shaidawa manema labarai cewa, an ɗauko wanda ake zargin ne a filin jirgin saman Malam Aminu jim kadan bayan ya sauko daga ƙasar Saudiyya a kano.

Muhuyi Magaji ya bayyana cewa wanda ake zargin yana amfani da Lamash a matsayin kamfani, ya sayar da filayen akan kudi kusan Naira Miliyan 2.5 kowannensu ga daidaikun mutane a Challawa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso.

Ya kuma sayar wa mazauna Garin Dawanau dake karamar Hukumar Dawakin Tofa filaye daban-daban.

“A yanzu haka muna kan binciken wanda ake zargin yadda Gwamnatin da ta shude ta ware masa filaye Guda 632, Kuma an sayar dashi ga mutane daban-daban a jihar,” inji Magaji.

Ya ƙara da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da shi a Gaban kotu.

Wannan sumamen wani Gagarumin ci gaba ne a yaki da cin hanci da Rashawa a jihar Kano.

Zargin sayar da filayen Gwamnati don amfanin kashin kai, babban laifi ne dake hana Jihar samun kuɗaɗen Shiga da ake buƙata. In ki Magaji.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *