Daga Baba Usman Gama
’Yan bindiga sun sako 1 daga cikin masu p} yiwa kasa hidima (NYSC) mata 7 da suka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.
Gamayyar jami’an tsaro sun yi nasarar kama mutane hudu da ake zargi da fashin bankuna a jihar Benue.
Ma’aikatan filin jirgin sama na Kano sun gudanar da zanga zangar lumana don nuna rashin jin dadi da wani gini da Rundunar Sojin Sama take yi a gaban gidajensu.
Mazauna Legas sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa.
Masu ruwa da tsaki wajen harkar jiragen sama sun ce Najeriya ta kai matsayin da za ta fara neman madadin man jirgi.
Yan sandan kasar Saliyo sun kama wani dan kasuwar Najeriya da ake nema ruwa a jallo, Nnanyereugo Best, kan kashe budurwarsa.
An sako tsohon shugaban ma’aikatan Shugaban Gabon Bongo bayan shafe kusan shekaru 4 a tsare
Shugaban Afrika ta Kudu Ramaphosa ya kwatanta yanayin da farar hula ke ciki a Gaza da bala’in da baƙar fatar ƙasarsa suka fuskanta lokacin mulkin wariyar launin fata.
Manchester City za ta bar ɗan wasan tsakiya na Ingila Kelvin Phillips mai shekara 27 ya bar ƙungiyar a watan Janairu mai zuwa.
Napoli na son tsohon kocin Brighton da Chelsea Graham Potter domin zama sabon kocin ƙungiyar, sai dai Potter na ciki ƙila wa ƙala game da Man. United idan Erik ten Hag zai bar ƙungiyar.
Ana hasashen Liverpool za ta ɗauki ɗan wasan Bayern Munich dan Jamus Jamal Musiala mai shekara 20.
EPL: Manchester United ta sami nasara akan Sheffield da ci 2:1 a wasan jiya.
EPL: Arsenal da Chelsea sun tashi 2:2 a wasan jiya.
Laliga: Atlentico Madrid ta sami nasara akan Celta Vigo da ci 3:0 a wasan jiya.
Laliga: Real Madrid da Seviilla sun tashi 1:1 a wasan jiya.
Bundesliga: Bayern Munich ta sami nasara akan Mainz da ci 3:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo