Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Juma’a 20/10/2023 – 05/04/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya bada umarnin biyan Malaman Jami’o’i albashin su da aka rike lokacin yajin aiki.

Shugaba Tinubu ya nada Adewale Adeniyi a matsayin Shugaban Kwastam.

Kashin farko na daliban Kano sun tashi a safiyar yau Juma’a zuwan kasashen waje kamar yadda Gwamnatin jihar ta yi alkawari.

Dala na ci gaba da hauhawa a kasuwannin bayan fage a Najeriya.

Hukumar NCDC a Nijeriya ta tabbatar da cewa mutum 9,478 sun kamu da cutar makarau a kananan hukumomi 137 na jihohi 20 da Abuja.

Gwamnan Katsina yace zasu kama sarakunan gargajiya dake taimakawa ‘yan ta’adda a jihar.

Gwamna Alex Otti na jihar Abiya ya samu nasara a Kotun ɗaukaka ƙara a Kano kan hukuncin babbar kotun tarayya na tsige shi da yan takarar LP.

Gwamna Dikko Radda na Katsina ya bukaci bai wa mutane damar siyan makamai kamar yadda ‘yan bindiga ke yi.

Mazauna Otukpo a jihar Benue sunyi gudun neman tsira bayan ‘yan fashi sun hari wasu Bankuna 2.

Firaministan Birtaniya ya gana da Shugaban Falasdinawa.

Bazoum ya musanta zargin tserewa daga Nijar.

Burkina Faso ta ayyana zazzaɓin Dengue a matsayin annoba.

An gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasɗinawa a Faransa.

Ramaphosa zai halarci taro a Masar kan rikicin Gaza.

An kashe kaji 45,000 a Mozambique bayan ɓullar murar tsuntsaye.

Guardiola yace Haaland ne ya kamata ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2023.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *