Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin tarayya tace za a jinkirta fara aikin sabbin jami’o’i da gwamnatin tsohon shugaba Buhari ta amince da kafa su.
Mummunan hatsarin mota a hanyar Potiskum ya yi ajalin mutane aƙalla 38, wasu kusan 50 na kwance a Asibiti a jihar Yobe.
Gwamnatin Zamfara ta kammala shirye-shirye domin gudanar da shagalin bikin mata marayu da ke zaune a gidajen marayu a garin Gusau, babban birnin jihar.
Sarkin masarautar Opokuma da ke ƙaramar hukumar Kolokuma/Opokuma a jihar Bayelsa, HRM King Collins Aranka, ya koka kan kuɗin alawus din wata-wata.
Mayakan Boko Haram 6,900 daga cikin wadanda suka mika wuya ne suka dawo cikin al’umma a cewar Gwamnatin Jihar Borno.
An gurfanar da Malamin makaranta da wasu 5 kan laifin sata a Osun.
Kotun Majistare da ke Dutse a Jihar Jigawa ta tsare jigon jam’iyyar APC a kurkuku, bisa zargin ɗirka wa ‘yar wanke wanken gidan sa cikin shege.
Dalibin jami’a ya rasu yana tsaka da rubuta jarrabawar karshe a jami’ar Gombe.
Daruruwan masu zanga-zanga sun yi sallah a wajen fadar firaministan Birtaniya.
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya amince da bude mashigar Rafah ga wasu manyan motoci kalilan dauke da kayan agaji zuwa Zirin Gaza.
Yaƙin Gaza: Masu zanga-zangar neman tsagaita wuta sun kutsa Majalisar Dokokin Amurka.
Turkiyya ta kama wata jagorar kungiyar ta’addanci ta PKK/KCK ta Norway.
Sojojin Brazil sun yi wa gwamnati gagarumar sata
Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a Jamhuriyar Congo.
‘Yan damfara sun saci kamannin shugaban Kungiyar AU.
Mohamed Salah ya bukaci kawo karshen ‘kisan kiyashin’ Gaza.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo