Takaitattun Labaran Duniya na Safiyar Laraba 11/10/2023CE – 26/03/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Gwamnatin tarayya ta ce ta na tunanin kafa kotu ta musamman da za ta saurari shari’ar rashin gaskiya da almundahana.

Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da shirin kwace haramtattun makamai a Filato, Bauchi da Kaduna.

Jami’an tsaro sun hallaka ‘yan fashin daji 67, sun ceto mutane 29 a Bauchi.

Rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta sanar da kama wasu mutane 3 da ake zargi da kashe dan Jarida, Hamisu Danjibga.

Wasu ‘yan fashi da makami sun aukawa wani bawan Allah a jihar Kwara, bayan ya fito daga Banki sunyi nasarar awan gaba da makudan kudi.

‘Yan bindiga sun sace dalibai a jami’ar Nassarawa

Cutar Diphtheria ta kashe yara 117 a Yobe.

Makwabta sun cafke wani wanda ya yi yunkurin yin fyade ga wata tsohuwa ’yar shekara 85 a yankin Uhronigbe da ke jihar Edo.

Kansilolin PDP sun sauya sheka zuwa APC a Kaduna.

Amurka ta soke tallafin Dala miliyan 442m da take ba wa Nijar.

Adadin mamata na karuwa a tsakanin dakarun HAMAS da na Izraela a Gaza.

Mazauna ƙauye sun cinye giwar da ta fito daga gandun daji a Congo.

Amurkawa 20 sun ɓata a Isra’ila.

Shugaban Majalisar Masallatan Harami, Sheikh Abdul Rahman Sudais, ya bayyana goyon bayansa ga Falasɗinawa tare da yin Allah-wadai da hare-haren Isara’ila a Zirin Gaza.

An ɗaure ƴar TikTok kan zagin shugaban ƙasa a Angola.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

One Reply to “Takaitattun Labaran Duniya na Safiyar Laraba 11/10/2023CE – 26/03/1445AH”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *