Takaitattun labaran duniya na Safiyar Lahadi 08/10/2023 – 23/03/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Atiku na neman kotun ƙoli ta ba shi damar shigar da sabuwar shaida kan Tinubu.

Mai fashin bakin siyasa, Farfesa Farooq Kperogi ya bayyana cewa Tinubu ya yi ganganci da ya mika takardar Difloma ga hukumar zabe.

INEC ta ta musanta zare hannu a ɗaukaka kara game da zaɓen gwamnan Kano.

Wani makaho mai maganin gargajiya mai suna Owolabi Adefemi wanda aka fi sani da Ojunu ya damfari wata tsohuwa Naira miliyan 19, kuma ya kwanta da ‘yarta da kuma jikarta a jihar Ogun.

Kungiyar PENGASSAN tace har yanzu gwamnatin Najeriya na biyan kudin tallafin man fetur.

Jami’an tsaro sun cafke wani matashi mai shekaru 30 da ya sare hannuwan mahaifiyarsa da adda saboda rashin jituwa a jihar Ogun.

Jam’iyyar NNPP a Kano ta ce babban kuskuren da Tinubu ya yi shi ne zaban Ganduje shugaban APC.

Jarumar fina finan Hausa ta Kannywood, Zuwaira Saleh Pantami wadda aka fi sani da Adama a cikin shirin Dadin Kowa, ta bayyana yadda aka yanke mata hukuncin kisa a Saudiyya.

Zuwa yanzu, alkaluman waɗanda suka mutu a harin Hamas ta kai Isra’ila ya kai 150, a cewar jami’an Isra’ila bayan garkuwa da wasu sojoji da fararen hula.

Sojojin Mali sun ƙwace wani gari a hannun ƴan a waren Tuareg.

Gwamnatin sojin Nijar ta zabtare kasafin kudin bana da kaso 40 cikin 100.

Sojojin da ke mulki a Gabon sun yi nadin mambobin majalisun dokokin kasar.

Dakarun Mali sun yi ikirarin kwato garin Anefis da ya jima a hannun ‘yan ta’adda.

Watakila Juventus ta ɗauki aron Jadon Sancho, a Janairu kafin ta saye shi gaba-ɗaya a bazara mai zuwa.

NPFL: Kano Pillars ta sami nasara akan Katsina United da ci 1:0 a wasan jiya.

Seria A: Juventus ta sami nasara akan Torino da ci 2:0 a wasan jiya.

Bundesliga: Dortmund ta sami nasara akan Union Berlin da ci 4:2 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *