Daga Nasiru Hassan Yalwa
Yayin da illahirin kasashen Turai da kuma kungiyarsu ta Tarayyar Turai (European Union) suka ce harin ramuwar gayyar da yau Asabar kungiyar Hamas ta kaddamar akan isra’ila wai hari ne na “ta’addanci,” wasu kasashen kamar Rasha da na musulmi sun bayyana sabanin haka.
Alfijir Labarai ta rawaito wasu daga cikin martanonin da wasu suka yi kamar yanda tashar talabijin din Aljazeera ya wallafa:
Kasar Egypt ko kuma Misra ta yi gargadi ne akan mummunan sakamakon da za a samu akan fadada tashin-tashina da zaman doya da manja a tsakanin isra’ila da Falasdinawa, cikin wata takardar manema labarai da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar.
Kasar ta yi kira da a kai zuciya nesa.
Iran: mai bada shawara ga Jagoran addini a kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyed Ali Khamenei, a madadin Iran ya ce, “Kasar Iran tana goyon bayan wannan kaddamar da hare-haren da Falasdinawa akan isra’ila, kamar yanda kamfanin dillancin labarai na ISNA ya wallafa.
“Muna taya mayakan gwagwarmayar Falasdinawa murna kan wannan nasara,” cewar Rahim Safawi, mashawarci ga Ayatollah Sayyed Ali Khamenei.
Sannan ya kara da cewa “Za mu ci gaba da taimaka wa Falasdinawa har zuwa ranar da za a ‘yantar da Falasdinu da birnin Kudus.”
Qatar: Ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta fitar da sanarwar manema labarai, inda ta ce isra’ila kadai za a zarga da laifin duk wani tashin hankalin da ke faruwa.
Sannan kasar ta yi kira ga dukkan bangarorin da su tsagaita wuta.
Daga karshe kasar ta Qatar ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakin taka wa isra’ila burki kar ta yi amfani da wannan damar domin kisan fararen hulan Falasdinawa a zirin Gaza.
Rasha: Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha, Mikhail Bogdanov ya ce Rasha tana tattaunawa da bangarorin na isra’ila da Falasdinawa da kuma kungiyar Larabawa domin a samu zaman lafiya.
Ya kara da cewa “A kowane lokaci muna kira zuwa ga samar da zaman lafiya,” kamar yanda kamfanin dillancin labaran The Interfax ya wallafa.
Saudi Arabia: ma’aikatar wajen kasar Saudiyya ta bukaci isra’ila da Falasdinawa da su dakatar da dukkannin rikici ba tare da bata lokaci ba.
“Muna bibiyar abinda ke faruwa tsakanin bangaren Falasdinawa da isra’ila wanda ya haifar da zazzafan rigima.”
Turkiyya: shugaba Recep Tayyib Erdogan ya bukaci Falasdinawa da isra’ila su kai zuciya nesa sannan su guji aikata abinda zai kara dagula zaman lafiya.
“Muna kira ga dukkan bangarorin da su kai zuciya nesa.
Dole su kauce wa rikici,” cewar Erdogan a yayin wani taro na jam’iyyarsa ta AK a birnin Ankara.
Hukumar Falasdinawa (PA): shugaban Hukumar Falasdinawa wato Palestinian Authority, Mahmoud Abbas ya ce “Al’ummar Falasdinawa suna da hakkin su kare kawukansu daga ta’addancin sojojin mamayan isra’ila,” a labarin da kamfanin dillancin labaran WAFA ta wallafa.
Shugaba Mahmoud Abbas ya maida wannan martani ne a wani taron gaggawa da ya gudanar da manyan jami’an gwamnatinsa a birnin Ramallah.
Hezbollah: Kungiyar gwagwarmaya ta Hezbollah da ke kasar Lebanon ta fitar da wata takardar manema labarai inda ta ce “Sau-da-kafa muna bibiyar abinda ke faruwa a zirin Gaza kuma kungiyar Hezbollah muna tattaunawa da shugabannin gwagwarmaya ta Hamas.”
Hezbollah ta kara da cewa “Wannan harin da Hamas ta kaddamar akan isra’ila wani mataki ne kwakkwara ya kamata.
Kuma abinda ya dace kenan matukar ana son a dakatar da mamayar kasar Falasdinu da isra’ila ke yi, kuma hakan wani sako ne zuwa ga kasashen Larabawa masu aniyar gyara hulda da isra’ila.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo
Assalamu Alaykum, alfijirlabarai.com sannunku da kokari agaskiya kuna matukar kokari wajen kawo mana sahihancin labari. Allah Ya kara taimako da kuma kara dafa maku. A bangaran harin da Palastin suka kai wa isra’il agaskiya yayi dai dai don an dade su isra’il suke ta zaluntar palastin kuma duniya sai tayi shiru amma yanzu tunda ita palastin ta rama, kasashen turai suna cewa ta’addancine. Gaskiya Qatar ta burge ne wajen fadin gaskia. Allah Ya kara taimakon musulunci da musulmai baki daya