Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta janye wasikar ta ta farko da ke nuna daukaka kara kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano.
Alfijir Labarai ta ruwaito cewa a wata wasika mai dauke da kwanan watan 6 ga watan Oktoba mai dauke da sa hannun Suleiman Alkali, shugaban sashin shari’a na hukumar a Kano, INEC ta ce ta janye karar da ta shigar saboda ba ta da dalilin daukaka karar akan duk hukuncin da kotun ta yi.
Hedikwatar hukumar ta umurce ni da cewa INEC a matsayita, ba ta da wani dalilin daukaka kara a kowane hukunci.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai a yammacin ranar Juma’a, Alkali ya ce an janye wasikar da aka rubuta wa kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano don daukaka kara.
Ya ƙara da cewa janye wasikar ya dace domin babu wani dalili a kan haka tun farko.
Amma ana iya fahimtar cewa akwai karfin fada a ji a lamarin.
Idan zaku tuna a ranar 20 ga watan Satumba, kwamitin alkalan kotun mai mutum 3 ya kori Gwamna Abba Yusuf tare da ayyana dan takarar jam’iyyar APC Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo