Gwamnatin Kano ta haramta amfani da wasu litattafai a Daukacin Makarantu Masu Zaman Kansu dana Sakai a Fa’din Jihar.
Alfijir Labarai ta rawaito hakan ya biyo bayan tunasarwa da bangarorin daban daban sukai kan wasu illoli da suke cikin Litattafan da ake ganin sunci karo da koyarwar Islama.
Hukumar Kulada Makarantu Masu Zaman Kansu ta fitar da Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Hamisu Muhammad, Daraktan Tsare-Tsare da Bincike a Madadin Mataimakin Gwamna kan Makarantu Masu Zaman Kansu Baba Abubakar Umar.
Litattafan sune kamar haka:
*The Queen Primer (all editions) A Royal Series Published by Nelson Publishers Limited
*Basic Science for Junior Secondary School, Razat Publishers, 2018 edition. (for JSS3).
*Active Basic Science, 2014 edition By Tola Anjorin, Okechukwu Okolo, Philias Yara, Bamidele Mutiu, Fatima Koki, Lydia Gbagu.
*Basic Science & Technology for Junior Secondary Schools 1, 2 and 3: By W.K Hamzat, S. Bakare.
*New Concept English for Senior Secondary Schools for SSS2, Revised edition (2018 edition) by J Eyisi, A Adekunle, T Adepolu, F Ademola Adeoye, Q Adams and, J Eto.
*Basic Social Studies for Primary Schools by BJ Obebe, DM Mohammed, S N Nwosu, J A Adeyanju and ah Carbin
Bugu da Kari Shugaban Hukumar Tace Fina Finai da Dab’i ta Jihar Kano, Abba Al Mustapha sunyi Nasarar kama tarin Littafin Queen Primer da Gwamnatin ta haramta koyar dashi a Fa’din jihar Kano.
A wani labarin kuma Olusegun Obasanjo Ya Bukaci Gwamnati Ta Tallafawa Masana’antu
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo