Wasu mutane dauke da makamai sun mamaye gidajen kwanan daliban jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsinma, FUDMA suka sace dalibai mata guda biyar.
Alfijir Labarai ta rawaito Lamarin da ya faru da misalin karfe biyu na daren Talata wayewar Laraba, ya faru ne a gidajen kwanan daliban da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri, a inda daliban suka kama gidajen da suke kwana.
Ya zuwa yanzu dai babu takamaiman bayanin asalin jihohi da kwasa-kwasan da azuzuwan da daliban suke. Kazalika, babu cikakken bayanin halin da daliban mata suke ciki a halin yanzu, don babu tabbacin ko ‘yan bindigar sun kira waya suna neman kudin fansa ko a’a.
Ko a kwanakin baya, wasu dalibai ‘yan jami’ar ta FUDMA sun taba fadawa irin wannan hali, inda wasu ‘yan bindiga suka yi awon-gaba da dalibai biyu.
Ko a makonni biyu da suka gabata, wasu ‘yan bindiga sun shiga jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau jihar Zamfara, inda suka sace dalibai mata masu tarin yawa. Sai dai bayanai sun ce an kubuto wasu daga cikinsu.
Sashen hulda da jama’a na jami’ar ta FUDMA bai kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba a hikumance.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta hannun mai magana da yawun ta ASP Sadiq Aliyu Abubakar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an kama mutum daya da ake zargi yana ba ‘yan ta’addar bayanan sirri, sannan an kama wasu mutane da dama da ake zargi da hannu a satar wadannan dalibai mata na Jami’ar FUDMA, Katsina.
Jami an tsaron sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike tare da tsaurara tsaro don ceto daliban da sauran mutane da ‘yan ta’adda ke tsare da su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb