Alakanta ƴaƴan NNPP Da Ta’addanci Da Mai Shari’a Anya yayi Jam’iyyar ta yi Allah wadai da kalaman


Babban mai bincike na jam’iyyar NNPP, Barista Ladipo Johnson, ya caccaki kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano, kan kalaman da kwamitin ya bayar ga jaridu na cewa magoya bayan gwamna Abba Kabir Yusuf da shugabancin jam’iyyar a jihar Kano, masu son tashin hankali ne kuma suna aikata ayyukan ta’addanci.

Alfijir Labarai ta rawaito cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas a karshen mako, Johnson ya nuna rashin amincewarsa da abin da ya bayyana a matsayin kokarin bata sunan magoya bayan jam’iyyar NNPP da na gwamnan jihar kano daga alkalan kotun.

Jonson ya nuna damuwa sosai sakamakon yadda a rubutun wani memba cikin alkalan mai shari’a Benson Anya ya yi Allah wadai da ‘yan jam’iyyar NNPP, wadanda ya kira su da “gungun masu sanye da jajayen hula wadanda suke abu kamar ‘yan kungiyar asiri da ‘yan ta’adda sune suka kore mu daga Kano suka sanya rayuwar mu cikin tsoro da firgici”.

Mai binciken na jam’iyyar NNPP ta kasa ya yi Allah wadai da kalaman Mai Shari’a Benson Anya na cewa, “Maimakon a bar wasu ‘yan siyasar Kano su yi amfani da ‘yan fashi da tashe-tashen hankula wajen kawar da dimokuradiyya a jihar Kano, za a yi amfani da adalci wajen hana su ruguza dimokaradiyya a Kano .

Jigon jam’iyyar NNPP ya yi kakkausar suka ga irin wadannan kalamai, wanda a cewarsa, bai dace da alkali kuma mai kare doka ba.

“Hakika, kalaman batanci, cin zarafi da tsinuwa da mai shari’a Benson Anya ya yi sun wuce ka’idojin shari’a, hakan ya nuna kamar yana da son wata jam’iyya, saboda yadda yake nuna kyama ga shugabanni, ’yan NNPP.

Ya nanata cewa jam’iyyar NNPP za ta ɗauki matakan da suka dace wadanda suka hadar da kai korafin su ga hukumar dake dake kula da Alkalai ta kasa NJC a kan kalaman da alkalin kotun ya yi.

Hakazalika za ta daukaka kara kan hukuncin da kotun ta yanke na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano, yana mai jaddada cewa jam’iyyar na da yakinin za a yi adalci a kotun daukaka kara. Kotu a lokacin da ya dace don karfafa imanin mutane a cikin shari’a da harkokin dimokuradiyya.

A karshe dai ta bayyana cewa abun da aka fada ba haka yake ba, domin gashi kotun bata yi adalci ba ta yanke hukunci ta manhajar’Zoom’ amma kuma babu wani abun na tashin hankali da ya faru a jihar kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *