Shugaba Tinubu ya magantu akan ɗaliban jami’ar Gusau

Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaron ƙasar su kuɓutar da sauran ɗalibai mata na Jami’ar tarayya da ke Gusau da masu garkuwa da mutane suka sace.

Mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar da wata sanarwa, Tinubu ya yi Allah wadai da sace ɗaliban da aka yi ranar Juma’a, yana mai cewa wannan abun rashin tausayi da imani kan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Tinubu ya jajanta wa iyalan waɗanda aka sacen, ya tabbatar da cewa a shirye gwamnatinsa take wajen kare duka ‘yan Najeriya, yana mai alƙawarta cewa za a yi duk mai yiwuw domin kuɓutar da ɗaliban.

Gwamnatin tarayya za ta tabbatar da bayar da kariya ga makarantu kasancewarsu cibiyoyin bayar da ilimi da ci gaban al’umma.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *