Jam’iyyar APC ta lashi takobin kama duk wani dan Najeriya mazauna amurka da ya yi zanga-zangar adawa akan Tinubu a amurkan.
Alfijir Labarai ta rawaito Yadda wasu yan Najeriya sun bayyana damuwarsu ga Jaridar Sahara Reporters cewa ana kokarin hanasu bayyana damuwarsu ta hanyar zanga-zangar da suka shirya yiwa shugaban kasar Najeriya a wani taro da zai gabatar a ranar 20 ga watan Satumba A birnin New York na kasar Amurka.

Da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, shugaban jam’iyyar APC reshen Amurka, Farfesa. Tai Balofin, ya yi ikirarin cewa wani dan jam’iyyar da aka dakatar, Adesegun Labanjo ne ya shirya taron.
A wani bangare sanarwar ta kara da cewa, “A kwanan nan ya zo mana cewa wasu mutane na shirin gudanar da wani gangami a ziyarar da shugaba Tinubu da ya kai Majalisar Dinkin Duniya.
Wannan gangamin da aka shirya kai tsaye ya mayar da martani ne ga taron da wani dakataccen Malam Labinjo ya shirya wanda ke ikirarin shi ne shugaban APC na kasa, a ranar 20 ga Satumbar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb