Gwamna Uba Sani Ya Nada Sabbin Manyan Sakatarori 19 Da Kara Wa’adin Wasu 7

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda 19 tare da tabbatar da 7 daga cikin tsoffin sakatarorin dindindin.

Alfijir Labarai ta rawaito Sabbin Sakatarorin Dindindin da ma’aikatun da aka tura su, ga su kamar haka:

Mukhtar Abdullahi – Ma’aikatar ci gaban Wasanni

Dorcas Inti Benjamin Iliya – Ma’aikatar Ayyuka da ci gaban Al’umma

Jummai C. Bako – Tsare-tsare karkashin ofishin Shugaban Ma’aikata

Jummai A. Danazumi Esq. – Ma’aikatar Shari’a

Rabiu Yunusa – Ma’aikatar Gidaje da raya birni

Ibrahim Sanusi – Hukumar Ma’aikatar kananan hukumomi.

Mansur Salanke Esq. – Ofishin Sakataren Gwamnati

Aishatu Abubakar Sadiq – Ma’aikatar Lafiya

Abdu Na Abdu Ashiru – Ma’aikatar ayyuka

Shehu Usman Salihu – Hukumar Ma’aikata

Habib A. Lawal – Ma’aikatar Kudi

Suwaiba Shehu Ibrahim – Hukumar jin dadin Malamai

Dr. Mahmud Lawal – ma’aikatar kula da kananan hukumomi

Linda Asabat Yakubu – ma’aikatar muhalli da ma’adinai

Ramatu MB Tukur – Hukumar kula da birnin Kaduna

Mohammed Hayatuddeen – Hukumar kula da birnin Zaria

Augustine Godwin Alex – Hukumar kula da birnin Kafanchan

Felicia Indoka Makama – Ofishin Gwamna

Al-Amin Murtala Dabo – Ofishin Gwamna

Sakatarorin dindindin guda 7 daga cikin tsoffin da aka tabbatar sun hada da:

Nuhu Isiyaku Buzun – Majalisar zartaswa da Harkokin Siyasa (CPA), Ofishin Sakataren Gwamnati.

Dr. Haliru Musa Soba – Ma’aikatar Ilimi

Dr. Yusuf Saleh – Ma’aikatar Kasuwanci, Ƙirƙira da Fasaha

Abubakar Abba Umar – Ma’aikatar Noma

Nasiru A. Banki – Ofishin Ma’aikata karkashin ofishin shugaban ma’aikata

Kabiru M. Mainasibi – Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida

Bashir Muhammad, mni – Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kudi

Gwamna Sani, ya bukaci sabbi da tsoffin sakatarorin dindindin din da aka nada da su nuna bajintar su cikin himma da gaskiya da adalci.

Gwamnan ya kuma nuna matukar godiyarsa ga daukacin sakatarorin dindindin din da ke barin gado bisa ga gudunmawar da suka bayar ga ci gaban jihar Kaduna, tare da yi musu fatan samun nasara a duk ayyukansu na gaba.

Leadership Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *