Aika-Aika Wata mata ta zane Alkali da bulala a Najeriya


Wata Kotun Majistare da ke zamanta a  Abakaliki Jihar Ebonyi, ta tasa keyar wata mata mai shayarwa ‘yar shekara 32, Misis Ann Akpa bisa zargin cin zarafin wani Alkali.

 Alfijir Labarai ta rawaito ƴan sanda sun gurfanar da Akpan Ann a gaban kuliya bisa zarginta da yi wa majistare Lilian Igwesi bulala da sanda a ranar 28 ga watan Agusta 2023 a lamba 32 Hill Top Road, Abakaliki.

 Wanda ake tuhuma a cikin karar tuhuma biyu mai lamba MAB / 630c/2023 an kuma zarge ta da haddasa rashin zaman lafiya ta hanyar zuba datti a cikin gidan majistare.

 Mai gabatar da kara na ‘yan sanda, ASP Chinagorom Eze, ta ce ta aikata laifukan da za a hukunta su a karkashin sashe na 335 da 249 (d) na kundin laifuffuka, Cap.  33, Juzu’i na 1, Dokokin Jihar Ebonyi, Nijeriya, 2009.

 Wadda ake tuhumar ta ki amsa laifuka biyun da ake tuhumarta da su na cin zarafi da haifar da rashin zaman lafiya.

 Lauyan wanda aka yi kara A. J. Uguru, Esq,  ya nemi a ba shi belin wanda ake kara, inda ya bayyana cewa laifin da ake tuhumata da su laifuka ne wanda ake iya bayar da beli.

Sai dai Alkalin kotun, Lynda Ogodo ta ki bauar da belin, ta kuma bayar da umarnin tsare ta a gidan yari na Abakaliki, sannan ta dage zaman Kotun zuwa ranar 27 ga watan Satumban 2023.

Isyaku.com

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

One Reply to “Aika-Aika Wata mata ta zane Alkali da bulala a Najeriya”

  1. Bansan Mai yahadasu ba kuma labarin Yanuna ba ta zaneta bane a matsayin alkaliya tunda ba akotu bane Amma wasu alkalan kam yakamata a zanesu nema amatsayin alkalan saboda rashin adalchin dasuke gudanarwa. Allah Yakyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *