Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya isa kotun sauraron kararrakin zabe yau Laraba.
A yau ne za a yanke hukunci kan kararraki uku da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da na jam’iyyar Labour, Peter Obi suka shigar a kan zaben shugaban kasa Bola Tinubu.
Shugaban kotun, Mai shari’a Haruna Tsammani ne zai yanke hukuncin a ranar Laraba, tare da taimakon sauran mambobin kwamitin-Alkalai Stephen Adah, Monsurat Bolaji-Yusuf, Moses Ugo, da Abba Mohammed.
Haka kuma, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje; da Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da Gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji; Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da Gwamnan Yobe; Mala Buni; da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma na daga cikin wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da suka isa harabar kotun domin shaida hukuncin.
Haka kuma an hangi wasu daga cikin jagororin jam’iyyar PDP ciki har da Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, da sauran su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
May Allah guide in discharging their constitutional obligation amen