Wani babban manazarci a cibiyar Tony Blair mai kula da sauyin duniya, Bulama Bukarti, ya ce mai yiwuwa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ba za ta yanke hukuncin da ake jira a ranar Laraba ba.
Kotun daukaka kara a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin din da ta gabata, ta ce a ranar Laraba za ta yanke hukunci kan karar da ke kalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Sai dai a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X mai taken: ‘Ba za a iya gabatar da HUKUNCIN ZABEN SHUGABAN KASA A GOBE’ Bukarti ya bayyana cewa yajin aikin da kungiyar kwadago ta kasa NLC ke yi na iya kawo cikas a harabar kotun.
Bukarti ya bayyana matsayar sa kan umarnin da kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya JUSUN ta bayar na rufe dukkanin kotunan kasar a yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.
Ya ce: “Ko zai yiwu yajin aikin NLC na gobe ya hana kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa yanke hukuncinta? Na yi imani yana da yiwuwar.
“Yayin da su kansu alkalan ba za su shiga yajin aikin ba, kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN) mai alaka da kungiyar NLC ta bayar da umarnin rufe dukkanin kotunan kasar yau da gobe.
“Idan hakan ta faru, zai haifar da rufe harabar kotun da ofisoshin alkalai, wanda hakan zai sa ba za a iya yanke hukuncin ba.
“Duk da haka, Kotun na iya jinkirta yanke hukunci har sai bayan yajin aikin, mai yuwuwa zuwa yammacin ko farkon dare.
“Amma wannan ba zai yi tasiri ba, domin JUSUN na iya kin bude kotun bayan awanni aiki ko kuma jami’an NLC na iya sanya ta a kulle har zuwa safiyar Alhamis.
Ina da sha’awar ganin abin da zai faru gobe,” lauyan ya kara da cewa.
Daily Nigerian
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM