Kotu Ta Saka Ranar Yanke Hukuncin Zaben Shugaban Ƙasar Najeriya

Kuma daidaiku ne, ciki har da lauyoyi da wakilan jam’iyyu za su samu shiga cikin kwayar kotun

Alfijir Labarai ta rawaito Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a 2023 da ya gudana, za ta yanke hukuncinta a ranar Laraba 6 ga watan Satumba kan korafe-korafen da aka shigar da ke kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu. 

Hukuncin da za ta yanke kan karar da jam’iyyar LP da dan takararta Peter Obi da PDP da dan takararta Atiku Abubakar da  APM da suka shigar suna kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu (APC) a matsayin shugaban Nijeriya.

A wata sanarwar da rijistan kotun daukaka kara Umar M. Bangari Esq ya fitar a ranar Litinin, ya ce wadanda aka tantance ne kawai za su samu shiga cikin kwaryar kotun. 

Ya kuma ce domin tabbatar da gaskiya da yin komai a bayyane, za a yada zaman hukuncin kai tsaye a gidajen talebijin na kasa domin al’umma su bibiya kai tsaye.

Sanarwar ta ce, “Kotun daukaka kara tana sanar da al’umma cewa za a yanke hukunci kan kararrakin da aka gabatar a gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a ranar Laraba 6 ga watan Satumba, 2023.

“Wadanda aka tantance ne kawai ke da ikon shiga harabar kotun.

“Kuma daidaiku ne, ciki har da lauyoyi da wakilan jam’iyyu za su samu shiga cikin kwayar kotun.”

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *