U K Mai Shayi Sun Tanadar Muku Nau’ikan Shayi Kala 37, Har Da Haɗin Ma aurata

Kamfaninmu ya shahara ne wajen samarwa al’umma nau’ikan shayi sama da kala 35, domin inganta Lafiyar al’umma da samun nutsuwa.

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban Kamfanin U K Maishayi Alh Ukasha Muhd Sani wanda aka fi sani da (U k Mai Shayi) ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawar sa da wakilinmu.

Mai Shayi yace wannan kamfani ya shahara ne wajen sayarda nau’ikan shayi wadanda ake samarda su daga kasashen Larabawa da Nijar da kuma kasashen Turawa.

Ya kara da cewa duk wani nau i na shayi Allah ya lamunce mana mukan iya binciko shi domin sarrafa shi, ya taimaki bayin Allah domin jin dadin bakinsu da kuma lafiyar jikinsu.

Muna da nau’ikan shayi wadanda muka gwada su muka kuma tabbatar da ingancin su kala talatin da 37, amma a ciki mun debo kusan kala goma sha biyu 12, sune muke bawa jama a a halin yanzu, ragowar kuma mun ajiye su sai a hankali zamu dinga fito da su da yardar Allah.

Kamfanin U k Mai Shayi a gaskiya babu irinsa duk fadin kasar nan wajen samar ya shayi zunzurutunsa.

Anan zan iya magana akan nau’ikan shayi kala hudu kawai 4.

  1. Green Tea
  2. Hylan Tea/Ahmar/Arebian Tea
  3. Shayin Goriba
  4. Shayin Gahwa
  5. Shayin Inibi
  6. Shayin Mango
  7. Shayin Pineapple
  8. Shayin Strawberry
  9. Shayin Abarba
  10. Shayin Na a na a

Ga mai neman karin bayani zai iya tuntubarmu a 07038210432 Kira ko Whatsapp ko kuma sakon imel akan sayukash@gmail.com

Idan muka ɗauki Green Tea, mukan sarrafa shi da wasu tsirrai da muke hada wa wadanda Allah ya hore mana, kuma ya yiwa mutum Basir, akwai yadda muke sarrafa shi yayi wa mutum maganin Urine Acid, akwai yadda shima muke yi ya yiwa mutum maganin kwalataras, sannan maganin Tayfod da Maleriy, hakazalika muna sarrafa shi ya yiwa mutum maganin rage kiba, da maganin karfin maza da mata su kansu, musamman ɗaukewar sha awar mata ko rashin ni’imarsu duk wannan yana samuwa ne daga Green Tea.

Hylan Tea a wajen Hausawa Larabawa su kira shi Ahmar Turawa kuma su kira shi Red Tea, shima Allah ya hore mana sun bincike muna sarrafa kala kala, musamman domin yayi dadi a baki kaji kamar karka bari, sannan muna ssarrafa shi domin ya yiwa mutum maganin Sanyi na infection, ko na ciwon gabobi, da tari da Mura, kai duk matsalar sanyi muna amfani da Hylan Tea domin magance wannan matsalar da izinin Allah.

Sai Shayin Goriba ita ma Allah ya bamu ikon sarrafata tayi wa mutum maganin Basir, ciwon shuga, Hawan jini da wankin ciki, da kuma shanta dan jin dadi, musamman zaka ci tuwo malmala ɗaya idan kasha shayinmu na goriba to insha Allahu za ka ci malmala biyu, domin zata saka bakinka ya yi ɗanɗano.

Sai shayin Gahwa inji Larabawa su kuma Hausawa su ce kalwar shayi, shima mukan sarrafa shi domin ya kara karfin jiki kuma ya hana bacci musamman masu ayyukan dare ko ya rage kitse, ko kuma mu sarrafa shi kaji kamar kana shan kofi.

Wadannan sune nau’ikan da zamu dan taba bayaninsu a wannan lokacin.

U k Mai Shayi ya kuma ce akwai albishir na musamman ga al’umma game da shayin inibi, domin mun yi bincike a kusan arewacin Najeriya babu wani wanda yake sarrafa shayin Inibi a gaskiya ko da dai ana yi to bai fito ba.

Shima kamfanin namu ya fara sarrafa shi babu wani hadi a cikinsa na flevior ko wani sinadari, shine zallarsa, idan kazo wajenmu zaka same shi.

Muna mai alfari da ayyukan mu wajen tabbatar da cewar duk shayin da aka gaya maka idan ka sha za ka tabbatar da cewar shine babu mis a cikinsa, kuma zaka shashi lafiya lafiya lau babu wata cutarwa ko kaji Canji a jikinka.

A bangaren shayin karfin maza da mata kuma, idan kazo mun san wanda zamu baka musamman idan shekarunka sun kai 40 zuwa kasa, akwai nasa haka suma 40 zuwa sama akwai irin nasu, haka masu ciwon shuga akwai kalar nasu batare da wata matsala ba, haka masu saurin inzali saurin biyan bukata ko kuma kana so ta kara kauri insha Allah muna da Tabbacin hakan da izinin Allah.

Hakazalika mata masu rashin ni’ima da ɗaukewar sha awa suma akwai nasu shayin zaki sha a nan kafin ki bar wajen, minti 30 ko 40 za kiji ya fara aiki, idan yayi miki sai ki biya, idan bai yi ba kiyi ta fiyarki.

Sannan kuma akwai shayin da yake maganin Infection na matan dai, insha Allah kika sha shina kwana 7, sai wani zancen kuma.

Bangaren zazzabin Typhoid da maleriya ko da su aka kawo ka wajenmu insha Allah kafin kabar wajen kana shan shayin zaka ji kayi zufa ya sauka, to idan ka sha na kwana 7 da yardar Allah zaka rabu da shi, amma idan wannan lokacin kasha kawai bamu da tabbacin warkewar sai dai dan abin da ba a rasa ba zai iya dawo a wani lokacin.

Bangaren ma aurata ma ba a barsu a baya ba, musamman matar da ta dade bata yi aure ba kuma bata tsalle tsalle, to bincike ya tabbatar mana da sha awarta tana daskarrwa ne, misali yadda kakide ko man shanu yake daskarewa idan babu zafi ko wuta, to itama sha awar matar da ta dade bata yi aure ba haka take.

To akwai albishir da mukewa ma aurata kan suyi sabis din jikinsu ta dawo yadda ya kamata, haka maza ma akwai nasu, musamman mukan basu shawara duk kwana 40, suyi sabis din jikinsu da wani nau in shayi, jikin dan adan kamar mota ce ko inji lokaci zuwa lokaci kana bukatar sabis a jikinka, wannan shayin zai maka maganin sanyi da infection da nokewar al aura da sauransu.

Kuma duk wannan bayanin farashin bashi da wani tsada, duba da Allah ne ya bamu ilmin da zama da kakanni, mukan samu masana itatuwa su shiga dawa su debo mana domin bawa jama a, shi yasa bama tsawwalawa domin idan ka matsa sai Allah ya barka da kayanka.

Kamfanin U K Mai Shayi yayi wani duba a dabia ta dan adam, mafi yawancin lokaci Shayi yana saka yunwa ko jin kwadayi, wannan yasa sai mukayi wata dabarar samar da abincin gargajiya kamar Danwake, Taliyar Hausa, Dankalin Turawa, Indomie, naman rago, naman kaza da naman kifi muna sarrafa shi kala kala, kuma idan kaci zaka ji yana da bambanci da wadanda ka saba ci a wasu wuraren, kokarinmu shine duk abinda za muyi muga an inganta shi domin samun ingantacciyar lafiya da dandano.

A kamfanin mu har yanzu muna amfani da daddawa da sinadaren girki na gargajiya da kuma amfani da maggi kadan, yadda kowa zai iya amfani da shi.

Shima a bangaren shayi muna amfani da sikari dan kadan ba kamar yadda mutane ke tsammani ba, sai abubuwa na gargajiya wadanda zasu baka dandano kamar sukarin, domin munyi bincike Sukari na ragewa magani karfi muddin za ayi amfani dashi sosai, shi yasa muka kirkiro hanyoyin da zamj dafa Shayinmu ba tare da mun tsawwala sukarin ba.

U k mai Shayi asalinsa a jihar Buachi ne daga nan muka je Jos, sai jihar Gombe, gashi yanzu haka muna Kano, kuma insha Allah nan ba da jimawa ba zamu dira Abuja da kaduna tare da jihar Katsina.

A Bauchi muna da reshe guda 4, a jihar.

  1. Randabau na Dogon Yaro GRA Yanyar Yalwa.
  2. CBN randabawod Lasfa Modern Market
  3. Gidan Salisu Gamayya, Sabil Plaza Maiduguri bypass
  4. GRA Randabod fire service kusa da Bauchi Club, shi wannan sabon wajen ne zamu bude U k mai Shayi Islamic Traditional Herbal store zamu bude na larabawa dana Turawa masu inganci.

Sai Kano a kan titin Audio Bako hanyar zuwa asibitin Nassarawa yana kallon Murtala suya Dantata Plaza.

Sai Garin Gombe muna nan a Bauchi Rd Uji Quarters kusa da yahuza Suya.

Sai kuma Jos shima a Bauchi Road a Mabo Plaza

Abin farin ciki kuma shine duk abinda muka lissafa cewar muna dashi, to ko a wane shagon namu zaka same shi.

Kuma duk inda kake a Najeriya da kasashen waje muna tura kayanmu cikin aminci.

Sannan kuma muna yiwa masu joint ko masu gidaje abinci albishir, zasu iya sarar wadannan shayin a wajenmu muna ruba su a jarkoki mu turaw musu da shi, duba da ba ko ina ne suke da wannan sirrin ba, kuma yana daukar kwanaki 21 da daya bai lalace ba kuma bai canja ba, muddin ba za a barshi a rana ba ko waje mai tsananin zafi ba insha Allah sai yayi sati 3 nan.

Ga mai neman karin bayani zai iya tuntubarmu a 07038210432 Kira ko Whatsapp ko kuma sakon imel akan sayukash@gmail.com

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *